1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Bush A Iraki

Ziyarar Bush a Iraki da janyewar sojan Birtaniya daga sansaninsu na nuni da wargajewar hadin guiwar kasashen biyu a kasar Iraki

Bush a Iraki

Bush a Iraki

Akwai wasu abubuwa na ban mamaki da kan faru, wadanda da wuya mutum ya amince da su. Askarawan Birtaniya na janyewa daga sansdaninsu na karshe a Basra dake kudancin Iraki. Sojoji 550 ke janyewa zuwa filin jiragen saman dake wajen birnin, suna masu bin dufun dare a asurce. Wannan canjin matsugunin tun da dadewa ne aka shirya yinsa domin kuwa sojojin Birtaniyar da suka ja daga a fadar Basra, tsofuwar fadar shugaba Saddam hussein, sun zama kamar fursinoni ne saboda ba su iya fita sakamakon barazanar hare-haren dakarun sa kai na ‘yan Shi’a. A daidai wannan ranar ce kuma shugaba Bush ya sulale zuwa lardin Anbar domin saduwa da sojojinsa. Kuma kamar yadda aka saba, ba tare da wata sanarwa ba ta yadda ‘yan jarida ba zasu samu ta cewa ba. Irin wannan ziyarar ba ta nuna cewar an kai ta ne ga wata kasa dake kan hanyar samun zaman lafiya. Amma akwai wasu abubuwa guda biyu dake tattare da wannan manufa dangane da Iraki. A game da Amurka, bisa ga dukkan alamu, kokarin shugaba Bush yake yi ya cimma daidaituwar baki domin tsayar da shawara akan makomar manufofinsa a Iraki, mako daya kafin babban kwamandan askarawan Amurkan ya gabatar da rahotonsa akan halin da ake ciki gaban majalisar dokokin Amurka. A cikin watan janairun da ya wuce ne shugaba Bush yayi gaban kansa wajen tsayar da shawarar tura karin sojoji dubu 29 zuwa Iraki yana mai fatali da adawar jam’iyyar Democrat. A ganinsa karfafa matakai na soja shi ne zai kai ga nasarar da aka yi tsawon shekaru hudu ana sauraronta tun bayan da Amurka ta kifar da mulkin Saddam Hussein. A cikin watan agusta kadai an halaka farar fula sama da 1800 sakamakon hare-haren kunar bakin wake da musayar wuta akai-akai. A yayinda shugaba Bush ke ci gaba da lalube a cikin dufu ita Birtaniya fara saduda tayi, inda take kokarin tara rundunar sojojinta su dubu biyar a waje daya. Ta dawo daga rakiyar maganar tabbatar da angizonta a wani yankin dake karkashin ikonta a kudancin Iraki. A takaice a yayinda Birtaniya ke kokarin canza wa sojojinta wurin zama, ita Amurka kokari take ta kara yawan sojojinta a daidai loikacin da al’amura ke kara tabarbarewa a kasar Iraki. Wannan maganar, kazalika a daya hannun tana mai yin nuni ne da barazanar da ake fuskanta a game da makomar hadin kan Amurka da Birtaniya, inda zamu iya cewar a yanzun dai wannan taron dangi ya watse kuma kowace daga cikinsu ta kanta take yi, in kuwa ana ta kai ba a ta hulla.