Ziyarar Bush A Brussels | Siyasa | DW | 22.02.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Bush A Brussels

A yau talata shugaba Bush ya gana da sauran shuagabannin kasashen kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels

Shugaba Bush a Brussels

Shugaba Bush a Brussels

Kafin a shiga zauren taron tsakanin shugaba Bush da sauran shuagabannin kasashen kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO, sai da aka ba wa sabon shugaban kasar Ukrain Viktor Yuschtschenko cikakkiyar dama ta gabatar da bayani a game da shirye-shiryensa na garambawul. Yuschtschenko ya ci gaba da nanata bukatar kasarsa ta Ukraine a game da samun karbuwa a kungiyar NATO da kuma Kungiyar Tarayyar turai. Ya ce Ukrain ba makobciyar kasa ba ce, ita ma bangare ce a nahiyar Turai. Sakatare-janar na kungiyar NATO Hoop Scheffer ya yaba da shugaban na kasar Ukrain, amma bai yi masa tayin samun karbuwa ba, inda ya ce a hakika kofar kungiyar a bude take ga kowace kasa ta nahiyar Turai dake bin manufofin demokradiyya tsantsa. Amma a wannan marra da ake ciki yanzun muhimmin abu shi ne a mayar da hankali wajen fadada yarjejeniyar kawancen dake akwai tsakanin Ukrain da kungiyar tsaron ta NATO. Kasar dai tana da sojojinta da dama a matakan kiyaye zaman lafiya a karkashin tutar NATO, kazalika da tsugunar da wata ‚yar karamar runduna da dakarun sojanta a Iraki. Za a janye wadannan sojojin nan ba da dadewa ba domin cika alkawarin da yayi wa jama’a a yakinsa na neman zabe a cewar Yuschtschenko. A lokacin ganawar tsakanin shugaba Goerge W. Bush da sauran shuagabannin kasashen kungiyar tsaron ta NATO, shugaban na Amurka yayi kira da a yi watsi da barakar da ta samu tsakaninsu sakamakon yakin Iraki, inda ya kara da cewar:

Kungiyar NATO wata kakkarfar shaida ce ta zahiri a game da alakar Amurka da kasashen Turai. A cikin jawabin da na gabatar jiya na yi nuni da cewar Amurka na bukatar wata kakkarfar nahiya ta Turai. Kuma da gaske nike a game da wannan batu.

To sai dai kuma kamar yadda wani jami’in diplomasiyyar Amurka ya nunar, kasar bata ga wani dalilin da zai sanya a kawo canji ga wannan alaka ko kuma a aiwatar da garambawul ga tsare-tsaren kungiyar ta NATO domin ba wa kawayen Amurkan a nahiyar Turai karin fada a ji ba. Amma fa ainifin wannan maganar ce shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya ba da shawara kanta lokacin taron tsaron da aka gudanar a Munich kwanaki goma da suka wuce. Shi ma sakatare-janar na kungiyar Hoop Scheffer na tattare da ra’ayin cewar lamarin na bukatar gyara. Bayan ganawar tasu dai akasarin shuagabannin kasashen kungiyar ta NATO sun tsunduma zuwa wani dandalin dabam a birnin Brussels, inda zasu sake ganawa da shugaba Bush a matsayinsu na shuagabannin kasashen KTT, nan ba da dadewa ba.