1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Bush a birnin Mainz na nan Jamus

Mohammad Nasiru AwalFebruary 24, 2005

Bush da Schröder sun sanar da ba juna hadin kai a batutuwa da dama bayan bambamce-bambamcen da suka samu a baya.

https://p.dw.com/p/Bvd0
Bush da Schröder a birnin Mainz
Bush da Schröder a birnin MainzHoto: AP

To yayin wannan ziyara da ya kai a birnin Mainz shugaba GWB yayi amfani da dukkan damar da ta samu wajen bayyana kyakkyawar abokantaka da Jamus. Shugaba Bush ya jaddada cewar ya zabi nahiyar Turai ta kasance wurin da zai fara yin rangadi a wa´adin shugabancinsa na biyu ne don tabbatar da irin kyawawan dangantaku dake tsakanin Amirka da Turai. Hakazalika ziyarar da ya kai birnin Mainz ta kasance mai muhimmanci a gareshi musamman bisa la´akari da muhimmancin huldar dangantaka tsakanin Jamus da Amirka.

"Burin mu iri daya ne wajen wanzar da zaman lafiya a duniya. Saboda haka Jamus wata babbar kawa ce ta wanzar da zaman lafiya da kuma ´yancin walwala."

Shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da shugaba Bush sun shafe awa daya suna tattauna akan batutuwan siyasar duniya. Ko da yake wannan ganawa ba ta yi tsawo ba, amma Schröder ya ce sun tattauna akan muhimman batutuwa musamman game da Iraqi, kuma ko wanen su ya bayyana matsayin sa.

"Ba mu yi wata rufa-rufa ba wajen bayyana bambamce-bambamcen da muka samu a baya, to amma yanzu duk sun zama tarihi. Manufar mu dai ita ce shimfida sahihiyar demukiradiyya a Iraqi."

Jamus dai ta ce zata ci-gaba da horas da sojoji da ´yan sandan Iraqi amma a wajen kasar. Bush ya mika godiyarsa ga wannan aiki da Jamus din ke yi. Shugaban na Amirka ya nuna shirin yin sulhu game da shirin nukiliyar kasar Iran inda ya ce:

"Kamar yadda na sha fada, matsayinmu shine zama kann teburin shawarwari. Amma ina yin tuni da cewar yanzu aka fara yunkuri na diplomasiya kuma Iran fa ba Iraqi ba ce."

Bush ya kara da cewar yana da muhimmanci Amirka da Turai su yi magana da murya daya wajen shawo kan Iran ta yi watsi da shirinta na samar da nukiliya.

Duk da sabanin da aka samu game da yarjejeniyar birnin Kyoto wadda Amirka taki amincewa da ita, amma ra´ayin Jamus da Amirka ya zo daya game da kare yanayin doron kasa, inji SG Schröder, sannan sai ya kara da cewa.

"Burin mu dai shine mu ba juna cikakken hadin kai a wannan fanni ba tare da ba da la´akari da yarjejeniyar Kyoto a matsayin wani makami mafi dacewa wajen kare muhalli ba."

Shugabannin biyu sun amince da wani gagarumin shirin kare yanayi doron kasa musamman ta bawa kasashe masu tasowa taimakon fasahohin samar da makamashi da baya gurabata kewayen dan Adam.

Bayan tattaunawar mista Schröder da uwargidansa Doris su gayyaci Bush da mai dakinsa zuwa cin abincin rana. Sauran ´yan siyasar Jamus ciki har da shugabar jam´iyar CDU Angela Merkel sun halarci wajen bukin cin abincin.

An dai dauki tsauraran matakan tsaro a cikin birnin Mainz da kewaye don hana masu zanga-zanga kimanin dubu 12 kutsawa wajen taron da ya gudana tsakanin Schröder da Bush.