Ziyarar Bush a Asia | Labarai | DW | 15.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Bush a Asia

A dazu dazun nan ne shugaba George W Bush na Amurka ya iasa kasar Japan don fara ziyarar aiki ta mako guda a yankin Asia.

Kasar dai ta Japan ta kasance zango na farko a cikin kasashen da shugaban na Amurka aka shirya cewa zai ziyarta a tsawon mako gudan..

Ragowar kasashen kuwa sun hadar da Koriya ta kudu da kasar Sin da kuma kasar Mongolia.

A dai kasar ta Japan an shirya cewa shugaba Bush zai yi ganawar keke da keke da shugaba Junichiro Koizumi a can birnin Kyoto, sai dai ba a fadi ajandar abubuwan da shugabbin biyu zasu tattauna ba.

Bugu da kari a lokacin ziyarar da zai kai izuwa koriya ta kudu, an shirya cewa shugaba Bush zai yi amfani da wannan dama wajen halartar taron kolin tattalin arziki na kasashen Asia dake yankin pacific da sauran kasashen dake yankin.