Ziyarar Bashar Assad a Rasha | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Bashar Assad a Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin a yau ya karbi bakuncin takawaransa na Syria Bashar Assad domin tattaunawa kan halinda ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

Wannan ziyara ta Assad ta biyo bayan tattaunawa tsakanin Putin da Firaministan Lebanon Fouad Siniora,wanda ya bukaci kasar Rasha data yi anfani da damar da take da ita akan Syria wajen taimaka inganta danganta tsakanin Lebanon da Syria.

Ana sa ran shugabannin biyu zasu tattauna hanyoyin kawo karshen tashe tashen hankula tsakanin Palasdinawa,tare da kokarin ganin an samu tattaunawar zaman lafiya tsakanin Israila da Syria.