1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Barak a Masar

December 26, 2007
https://p.dw.com/p/CgRh

Ministan tsaron Israila Ehud Barak zai kai ziyara a ƙasar Masar inda zai tattauna tare da Shugaba Hosni Mubarak da wasu manyan jamian tsaro na kasar. Karon farko kenan da Barak zai je Masar tun daga lokacin da ya kama aiki a watan Yunin da ya gabata. Za su tattaunawa a wurin shakatawar nan na Sharm al-Shaikh, a daidai lokacin da ake ce ce ku ce akan yin fasakaurin makamai daga Masar zuwa Zirin Gaza. Ana sa rai Barak zai nemi Masar da ta binciki yin smogan makaman daga hamadar Sinai zuwa zirin Gaza, dake ƙarƙashin ikon ƙungiyar Hamas tun watan Yunin da ya gabata. Ƙasar Masar ta taka rawa wajen neman sakin sojar Israila mai suna Gilad Shalit da mayaƙan Gaza suka cafke a watan Yunin bara da har yanzu yake tsare.Ana sa rai Israila zata yi musayar wannan soja da firsinonin falisdinu guda 450.