Ziyarar Ashton a Gaza | Siyasa | DW | 18.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Ashton a Gaza

Jami'ar kula da harkokin wajen EU Catherine Ashto ta kai ziyara a Gaza

default

Catherine Ashton

A ziyarta ta farko a Gabas ta tsakiya jami'ar kula da harkokin waje na EU Catherine Ashton, a yau ta kai ziyara a Zirin Gaza wanda yake killace tun lokacin da Hamas ta karɓi iko. Ashton za ta gabatar da manufar EU na bada tallafin kuɗi don agazawa al'ummar yankin, waɗanda suke matuƙar buƙatar agajin gaggawa. Ana saran kuma Ashton za ta gana da wakilin MDD duniya dake kula da 'yan gudun hijira wanda yake a birnin Gaza. Kusan a dai dai lokacin da Ashton take isa zirin Gaza don kai ziyara, sai gashi an harba wata roka daga Gaza izuwa kan iyakarsu da Isra'ila, wanda kuma ya yi sandiyar mutuwar wani manomi ɗan ƙasar Thailand. Kafin hakan ma dai, ajiya wasu rokoki biyu ta aka harbo daga yankin na Gaza sun faɗa cikin ƙasar Isra'ila, amma dai babu wanda suka raunata. Catherine Ashton dai ta gana da shugaban Isra'ila Shimon Perese, kuma ta bayyana cewa ƙungiyar EU tana buƙatar lallai a koma kan tattauna ta haƙiƙi tsakanin Yahudawa da Palsɗinawa, domin samun zaman lafiya. Ashton tace batun gina matsunan Yahudawa da Isra'ila takeyi yana matakar kawo koma baya a tattaunar da ake buƙata, inda ta ƙara dacewa. "Shawara ta anan itace, hanya mafi sauƙi ta samun zaman lafiya shine a mutunta buƙatun Yahudawa da Palasɗinawa, kuma a ɗauke su da mahimmanci. Ina ganin daɗaɗɗiyar buƙatar Palasɗinawa, itace su samu gwamnati mai 'yancin kai wanda za ta haɗa dukkan Palasɗinawa. Kana yin haka da wuri shine abu mafi a'ala a gare mu". Da yake maida martini ministan harkokin wajen Isra'ila Avigdor Liebermann, wanda yake tsaye a gefen Ashton ya bayyana cewa taƙaddama da aka samu tsakanin Isra'ila da Amirka, bisa gina ƙarin matsunan Yahudawa a gabashin birnin Ƙudus dole a warwareta. #1# "Ina ganin muna iya duk ƙoƙarinmu, na kaucewa ja in ja walau dai tsakanin da Amirka ko Tarayyar Turai ko kuma ƙasashen dake shiga tsakanin a tattaunawar gabas ta tsakiya. Muna bin yanyoyin da muka saba, domin bayyana matsayin mu. Kuma muna fatan za'a fahimci juna. Amma bana fatan ƙara ruruta wuta, bisa abinda ke faruwa a yanzu" Ita dai jami'ar kula da Ketare ta ƙungiyar EU a ziyar ta ta, ta buƙaci da Isra'ila da Palsɗinawa, da su ɗau dukkan matakan da za su ɗauka, domin komawa kan teburin shawari batare da bata lokaci ba. Matsayin Firayim minista Benjamen Netanyahu da majalisar tsaron ƙasar dai bata sauya ba kan matakin gina mtsuƙunan Yahudawa. Kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka rawaito,Sai dai kawai Yahudawan na laluɓo amsar da za su baiwa Amirka, bisa buƙatar komawa kan tattaunawa tsakaninsu da Palasɗinawa. Mawallafa: Clemens Verkotte da Usman Shehu Usman Edita: Amhadu Tijjani Lawal