1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Archbishop Zollitsch a Nigeria

September 11, 2009

Archbishop Robert Zollitsch na majami´ar Katholika a Jamus ya nuna gamsuwa da ziyarar da ya kai tarayyar Nijeriya

https://p.dw.com/p/JcxE
Archbishop Robert ZollitschHoto: picture alliance / dpa

A ƙarshen mako ne Archbishop Robert Zollitsch na majami´ar katholika a Jamus ya kammala ziyarar kwanaki 10 da ya kai tarayyar Nijeriya inda ya gana da shugabannin addinan Kirista da na Musulunci da kuma sarakunan gargajiya na faɗin ƙasar baki ɗaya a wani mataki na ƙara fahimtar juna da inganta zaman lafiya tsakanin al´ummomin wannan ƙasa mafi yawan al´umma a nahiyar Afirka.

A taron manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, Archbishop Robert Zollitsch ya bayyana dalilinsa na zuwa Nijeriya da cewa wannan ziyara ita ce irinta ta farko da ya kai nahiyar Afirka baki ɗaya. Tarayyar Nijeriya mai yawan al´uma kimanin miliyan 140 yawan musulmai a ƙasar ya yi daidai da na kiristoci. Duk da kyakkyawan zaman cuɗe ni in cuɗe ka da fahimtar juna da ake samu a tsakaninsu, amma lokaci lokaci akan fuskanci rashin jituwa tsakanin mabiya waɗannan manyan addinan biyu a tarayyar ta Nijeriya. Duk da ƙoƙarin da hukumomi da shugabannin addinan ke yi na ƙara wayar da mabiyansu kai, wasu ɓata gari na ci-gaba da cusa ra´ayoyin rashin fahimta tsakani don cimma wani buri na daban. Ganin yadda rigingimun ke aukuwa lokaci zuwa lokaci, Archbishop ɗin ya ƙuduri aniyar zuwa Nijeriya domin ba da ta sa gudunmawa wajen samun fahimtar juna tsakanin kiristoci da musulman wannan ƙasa. Tun gabanin ziyarar ta sa Archbishop Zollitsch ya kwatanta Nijeriya a matsayin wata ƙasa da addinin ke janyo ɓaraka tsakanin al´umarta, saboda haka yake da muhimmanci a fito fili a tattauna da juna.

“Babu zaɓi da ya fi tattaunawa da juna. Abu mafi ɓacin rai a gareni shi ne yadda wasu mutane ke amfani da addini suna cusa gaba da rigingimu tsakanin mutane. Manufar addinai ita ce samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al´umma. Wannan shi ne alhakin da ya rataya wuyanmu. Idan na samu ƙarfin guiwa da ikon ba da tawa ´yar ƙaramar gudunmawa wajen samar da zaman lafiya, to zan ce kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu dangane da ziyarar da na kai Nijeriya.”

A zangon farko na rangadin jihohin Nijeriya, Archbishop Zollitsch ya ziyarci garin Onitsha na jihar Anambra inda ya gana da bishop-bishop da sarakunan gargajiya na wannan jiha da ma na yankin Niger Delta baki ɗaya.

Zollitsch ya bayyana fahimtarsa game da mu´amalar da ya gani a ziyararsa ta yankin Niger Delta da kuma shiyar Onitsha dake kudu maso gabashin Nijeriya.

Reverend Father Mathew Ndibey ya bayyana zuwa Archbishop ɗin da cewa abin ya bawa ce matuƙa sannan kuma yayi kira ga al´ummar musulmi da kiristoci a Nijeriya da su ci-gaba da zaman lumana da juna.

A can birnin Kaduna dake arewacin Nijeriya an yiwa Zollitsch kyakkyawar tarba inda yara ƙanana na cocin katholika a Kaduna suka rera waƙar yi masa maraba.

A Kadunan Zollitsch da sauran bishop bishop na birnin sun yi rangadin wurare da dama inda suka gana da shugabannin musulmai a wani mataki na ƙara fahimtar juna da samun lumana a tsakani. Bishop Matthew Manoso Danguso shi ne babban shugaban ´yan Katholika a Laduna, ya bayyana hulɗar dangantaku dake tsakaninsu da takwarorinsu na Jamus da cewa abin yabawa ne.

A ziyarar da ya kai garin Jos Zollitsch ya gana da sarakunan gargajiya na musulmai da Kirista tare da shugabannin addinai. A jawabin da ya gabatar shugaban na ´yan katholika a Jamus ya nuna matuƙar baƙin cikinsa yadda jama´a kewa addini mummunar fahimtar, ya ce babban abin da addinin Kirista da musulunci suke koyarwa shi ne zaman lumana da juna don haka babu hujjar riƘa kashe juna tsakanin mabiya addinan biyu, inda ya yi nuni da irin kyakkyawar zamantakewa ta musulmi da kirista a Jamus.

Babban Archbishop na Katholika dake Jos Ignatius Kaigama ya ce tun ba yau ba al´umar Jamus ke taikamawa al´umar jihar Filato kuma wannan dangantaka ta kai ga zuwa babban baƙon.

Daga cikin waɗanda suka halarci ganawar a Jos har da Sarkin Wase Dr. Haruna Abdullahi wanda ya jaddada farin ciki da goyon baya na al´umar musulmi wajen ganin an cimma zaman lumana tsakanin al´ummomin musulmi da kirista a jihar Filato baki ɗaya.

Archbisop Zollitsch ya gamsu da ziyarar da ya kai a tarayyar ta Nijeriya inda a hira da DW ya ce ko shakka babu kwalliya ta mayar da kuɗin sabulu.

“Na kai ziyara wata babbar ƙasa mai ɗimbin arziki amma ɗaukacin al´umarta na fama da talauci. Abin da ya burge ni shi ne yadda jama´a ke maraba da juna. Na gamsu da tattaunawar da na yi da shugabannin addinai. Muhimmin abu shi ne ba kawai kira ga jama´a da su yi imani da Allah ba, a´a dole ne a yi musu adalci a kuma samu zaman lafiya tsakani. Wannan shi ne saƙo na na ƙarshen azumin watan Ramadan.”

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal