Ziyarar Angela Merkel a yankin Gabas Ta Tsakiya | Labarai | DW | 29.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar Angela Merkel a yankin Gabas Ta Tsakiya

A yau lahadi SGJ Angela Merkel zata fara wata ziyarar aiki ta yini biyu a Birnin Kudus da kuma birnin Ramallah na Falasdinawa. Cin zaben da Hamas ta yi a yankunan Falasdinawa shi zai mamaye tattaunwar da Merkel zata yi a lokacin wannan rangadi na yankin GTT. Da farko dai zata gana ne da FM Isra´ila Ehud Olmert wanda ke tafiyar da harkokin mulki a madadin Ariel Sharon mai fama da rashin lafiya. Baya ga zaben da aka gudanar a yankunan Falasdinawa, wasu batutuwan da za´a mayar da hankali kai a tattaunawar da zasu yi sun hada da shirin nukiliyar Iran da ake takaddama a kai wanda kuma ya shafi Isra´ila kai tsaye. A gobe litinin zata gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a birnin Ramallah.