1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar aiki ta shugaban kasar Chadi a Najeriya.

Ubale MusaMay 11, 2015

Mahimman batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna a kai, sun hada da yaki da ta'addancin da ya mamaye kasashen yankin tafkin Chadi, da kuma neman mafita.

https://p.dw.com/p/1FOE7
Nigeria Treffen Idriss Déby & Goodluck Jonathan
Hoto: DW/U. Musa

Duk da cewar dai ya ce ya iso Abuja da nufin jinjinawa zaben da ya shude, mafi daukar hankali ga ziyarar ta Idriss Deby Itno a Tarayyar Najeriya na zaman rikicin Boko Haram da ya-ki ci ya-ki cinyewa a cikin tafkin Chadi a halin yanzu. Kama daga labarin 'yan mata 'yan makaranta na Chibok, ya zuwa maboyar Abubakar Shekau dama sojan hayar Africa ta kudu dai tambayoyi sun cika bakunan masu takama da jarida da suka kalli kasancewar Idris Deby a matsayin damar da babu irinta. Tun da farkon fari Deby da ke samun rakiyar manyan jami'an gwamnatin kasar ta Chadi mai tasiri a cikin yakin, ya share tsawon awa guda yana ganawa da Shugaba Jonathan da manyan jami'an tsaron Najeriya kafin daga bisani ya amsa tambayoyin 'yan jarida. Game da makomar Abubakar Shekau dai Deby ya ce bai sani ba a yanzu duk da cewa karfin kungiyar ya yi kasa.

Kokarin samar da tsaro a tafkin Chadi.

Flucht über den Tschadsee
Hoto: picture-alliance/dpa/Palitza

" A baya dai an ruwaito Shugaba Deby na fadin ya san inda shugaban kungiyar ta Boko Haram ke buya, tare da nemansa ya mika kansa ko kuma a cimmasa komai daci a bangaren na Chadin da ake yiwa kallon kashin bayan nasarar da sojan kasar ta Najeriya ke ikirarin samu yanzu. Wani abun kuma da ya dauki hankali a ziyarar Shugaban na Chadi, na zaman kasancewar tsohon gwamnan Jihar Borno Ali Madu Sharif a cikin tawagar kasar ta chadi. A baya dai Sharif din ya sha karyata zargin kasancewar hannunsa a cikin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban al'ummar kasashen tafkin Chadi tare da hargitsa lamura a cikinsa.

Tschadische Soldaten bei Rückkehr aus Mali 13.05.2013 mit Präsident Idriss Deby Itno
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Chadi na taka rawar gani a yaki da Boko Haram

Wannan karo na biyu da Sharif din ke zama cikin tawagar da a baya ta kalleshi da taka rawa a ziyarar Shugaba Jonathan zuwa birnin Njamena na kasar Chadi. Ziyarar Shugaba Deby dai ta zamo wata dama ta baiyyana wani shirin kafa runduna guda a bangaren kasashen yankin hudu da zata rikide ya zuwa rundunar kota kwana ta nahiyar Afirka kuma ta taka rawa a tabbatar da zaman lafiyar daukacin yankin

"Kasashen tafkin Chadi na shirin kafa rundunar hadin gwiwar da za ta rikide zuwa rundunar ko ta kwana a kasashen nahiyar Africa da za ta yi aikin kare yankin."

Majiyoyi dai sun ce mahukuntan na Abuja na cikin tsaka mai wuya a yakin da suke kallon karshensa kusa amma kuma ba su da kudaden ci gaba da biyan sojan hayar kasar Afirka ta Kudu da ke jan ragamar yakin.