1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Yayi Boni a Liberia

Yahouza S.MadobiAugust 9, 2007

Shugaban ƙasar Benin T.Yayi Boni ya kammalla ziyara aiki a Liberia

https://p.dw.com/p/Btum
Hoto: dpa - Report

Shugaban ƙasar Benin Thomas Yayi Boni ya kai ziyara aiki a Liberia, inda ya gana da takwarar sac, Ellen Searlef Johson a game da batutuwa daban-daban da su ka shafi mu´amila tsakanin Benin da Liberia, da kuma yankin yammancin Afrika baki ɗaya.

A ƙarshen wannan ziyara ta yini ɗaya, Thomas Yayi Boni da Ellen Searlef Johson, sun kiri taron manema labarai na haɗin gwiwa, domin bayyana sakamakon da su ka cimma.

Mahimman batutuwan da su ka da su ka tantana akai sun haɗa da m´amilar saye da sayarwa tsakanin ƙasashen 2, dukan su membobi a ƙungiyar haɓɓaka tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika wato, ECOWAS ko kuma CEDEAO.

Thomas Yayi Boni ya tsokaci a game da ɗimbin bashin da ƙasashen da ƙungiyoyin na dunia su ka tambayo Liberia wanda yawan shi ya kai dalla milion dubu 14.

A cewar shugaban ƙasar Benin wannan bashi yayi yawa ga ƙasar da ta yi fama da yaƙin bassasa na tsawan shekaru 14.

A game da haka, ya ce a shire ya ke ya kamawa Liberia wajen faɗakar da dunia a game wajibcin yafe wannan bassusuka, domin baiwa hukumomin Monrovia damar tada komaɗar tattalin arzikin ƙasar.

Kazalika ya yi yabo da jinjina dantse, ga Ellen Searlef Johnson a game da kyakyawar rawa da ta taka tun lokacin da ta hau kan karagar mulki, wajen warware matsaloli daban-daban da su ka dabaibaye ci gaban ƙasar Liberia.

Ya zuwa yanzu Liberia bisa jagorancin Searlef Johnson ta hau turtbar ci gaba mai inganci inji shugaban ƙasar Benin ta la´akari da ɓalle takunkumi sayar da lu´lu´lun kasar a kasuwanin dunia, da kumna tallafi da Liberia ke samu daga ƙasashe masu hanu da shuni, wanda a sakamakon hakan, Liberia ta fara farfaɗowa daga bila´in yaƙi.

A game da halin da ake ciki ta fannin tsaro a yankin yammacin Afrkira, shugabanin sun 2 ,sun bada haɗin kai ga yunƙurin samar da zamam nahia mai ɗorewa a ƙasar Cote D´Ivoire.

Sanarwar haɗin gwiwa, da su ka sa ma hannu, ta nunar da cewa, yarjeniyar da aka cimma tsakanin yan tawaye da dakarun gwamnatin Cote D´Ivoire,a Birnin Ouagadougou na Burkina Faso,ranar 4 ga watan maris da ya wuce, ita hanya mafi dacewa ta kawo ƙarshen rikicin tawaye a Cote D´Ivoire, saboda haka, sun bayyana mahimmancin aiki sau da ƙafa da matakan da wannan yarjejiya ta tanada.

Boni da Johson sun yi lale marhabin da sanarwar shugaba Lauran Bagbo, ranar litinin da ta gabata.

Albarkacin zagayawar ranar samun yancin kann Cote D´Ivoire, shugaban Bagbo, ya ce a shirye ya ke a gudanar da zaɓɓuɓuka a watan desember na wannan shekara.