Ziyara yan majalisar turai a Darfur | Labarai | DW | 05.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara yan majalisar turai a Darfur

Yan majalisun ƙungiyar gamayya turai, sun bayyana sanarwa, a game da halin da ake cikin a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

A sakamakon ziyara aikin da wakilan EU su ka kai a wannan yanki, sun ganewa idanun su matsanacin halin da al´ummomi ke ciki.

Shugabar tawagar yan majalisun tarayya turai, Josef Borrel ya sanar manema labarai cewar, yarjeniyar zaman lahia da a ka ratabawa hannu, a shekara da ta gabata, ba ta tsinana komai ba, wajen maido da kwanciyar hankali, a Darfur, inda har yanzu ƙungiyoyin tawaye ke cin karen su babu babbaka.

Tawagar ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Dunia, ta gaggauta aika rundunar ƙasa da ƙasa wadda a ka cimma daidato kanta tare da amincewar hukumomin Khartum.