1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara wakilin Majalisar Dinki Dunia a kasar Kote Divoire

Yahouza sadissouOctober 18, 2005

Shugaban komitin laddabtarwa na Majalisar Dinkin Dunia ya kai ziyara a kasar Kote Divoire

https://p.dw.com/p/Bu4p

Yau ne shugaban komitin ladabtarwa, na Majalisar Dinkin dunia Adamantios vassilakis ya fara ziyara aiki ta tsawon kwanaki 3, a kasar Kote Divoire.

A tsawan wannan kwanaki, shugaban, zai gana da Lauran Bagbo, da kuma Praminstan rikwan kwarya, Seydu Diara, da membobin gwamnatin sa, da shuwagabanin kungiyoyi daban daban.

A daya hannun wakilin na Majalisar Dinkin Dunia, zai tantana da jikadodin kasashe membobin komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, da ke kasar Kote Divoire, da shugaban majalisar dokoki Mamadu Kulibaki, da tsofan shugaban kasa Henri konan Bedie.

Adamantis zai kai ziyara a yankin arewancin kasar, inda zai sadu da shugabanin yan tawaye.

Mahimman burrurukan da ake sa ran cimma a wannan ziyarce- ziyarce, su ne na bitar nasarori, da akasin, da a ka samu bisa yunkurin shinfida zaman lahia, a kasar Kote Divoire, da ta fada rikicin tawaye tun watan satumber na shekara ta 2002.

Tun watan november na shekara ta 2004 komitin sulhu na Majlisar Dinkin Dunia,ya rattaba hannu a kan kuri´ar amincewa da saka takunkumi ga kasar Kote Divoire , da kuma daukar matakan hukunta duk wanda a ka samu da hannu a walwale tunkar da ke, ta fannin magance rikicin wannan kasa.

Komitin suklhu ya girka wani komiti bisa jagorancin Adamantis Vassilakis, wanda a ka azawa yaunin, tabbatar da cika wannan umurni na majalisar Dinkin dunia.

Ziyara ta jami´in na Majlisar Dinkin Dunia, na wakana a daidai lokacin da shugaban yan tawayen Kote Divoire Guillaume Soro, ya bayyana bukatar rudunar tawayen FN, ta samun kujera saban Praministan rikwan kwarya.

Ranar juma´a ce da ta wuce Majalisar Dinkin Dunia, ta bada goyan baya, ga shawara Kungiyar tarayya wacce ta tanado cewa, shugaban Lauran Bagbo ya ci gaba da rike ragamar mulkin kasdar, har tsawan shekara guda, kamin a shirya saban zabe, haka zalika a nada saban Praminista, wanda zai samu hadinkai daga bangarorin daban-daban na siyasa.

A cewar Guillaume Soro, wajibi saban Praministan ,ya fito daga yankin Arewa, da yan tawaye ke ikre da shi, muddun a na bukatar samun hadinkan kasa.

Tun bayan da kungiyar Taraya Afrika ta bayyana wannan shawara kafofin sadarwa na kasar, su ka fara hasashen wanda za a nada a mukamin saban praministan

Sunayen da su ka fi ambatta sun hada da na Charles Konan Bani gwamnan haddadiyar bakin kasashen Afrika ta yamma, da kuma Amara Aissy, shugaban hukumar gudanarwa na farko, ta kungiyar taraya Afrika.

A wani labarin kuma, da ya shafi kasar Kote Divoire, ministan tsaro ta Fransa Mishel Aliot Marie, ta sabke shugaban rundunar shiga tsakani ta kasar Fransa da ke Kote Divoire Jannar Henri Poncet daga mukamin sa, tare da wasu karin manyan sojoji 2 membobin tawagar rundunar Licorne a Kote Divoire.

Ministan Tsaron ta dauke wannan mataki, domin hukunta sojojin a kan abinda ta kira rufa rufa da su ka yi, a game da mutuwar wani dan kasar Kote Divoire, da sojojin Fransa su ka bindige ranar 17 ga watan mayu da yawuce.

Jannar Elrick Irastorza ne, ya cenji Jannar Poncet a wannan matsayi, inda zai jagoranci rundunar Licorne ta Fransa a Kote Divoire da ta kunshi sojoji dubu 4.