Ziyara Vladmir Poutine a China | Labarai | DW | 21.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Vladmir Poutine a China

Shugaban ƙasar Rasha Vladmir Poutine, ya fara ziyara aiki ta kwanaki 2, a ƙasar China.

A na sa ran, a sakamakon wannan ziyara, ƙasashe 2, su rattaba hannu a kan yarjeniyoyi, kimanin15, ta fannin cinakin makamashi.

ƙasar China ,da ke ta 2 a dunia, ta fannin anfani da man petur, na bukatar ƙara faɗaɗa odar mai, daga Rasha.

Sannan Rasha na bukatar rage dogaro da ƙasashen turai, a sayar da iskan Gaz.

Albarkacin wannan ziyara,Kampanin Gazprom, na Rasha zai rattaba hannu, a kann yarjenejiya cinikaya, da takwaran sa, China National Petrolium Corp.

Hukumomin Pekin na ɗaukar wannan ziyara, a matsayin wata babbar dama, da cima burin su, na shinfiɗa bututun man petur, daga yankin Siberia na Rasha, zuwa China.

Hulɗoɗi tsakanin Rasha da China, na ci gaba da inganta saboda gurin ƙasashen 2, na taka birki, ga manufofin Amurika, a nahiyar Asia.

Shugaba Vladmiri Poutine, da takwaran sa, Hu Jin Tao, za su anfani da wannan dama, domin masanyar ra´ayoyi, a game da siyasar dunia, mussaman rikicin makaman nukleyar Iran.

Rasha da China, ƙasashe 2, masu faɗa aji, a dunia na nuna goyan baya, ga hukumomin Teheran, a kan rikicin na makaman nuklea.