Ziyara Tony Blair a yankin gabacin turai
December 1, 2005Talla
Yau ne Praministan Britania Tony Blair, bugu da kari shugaban kungiyar gamayya turai, ya fara rangadi a yankin gabashin turai.
Blair zai tantanawa da sabin kasashe membobin Eu a kan batun kassafin kudin kungiyar, da har yanzu a ka kasa tsaida wa.
A mataki na farko, zai sadu da shugabanin kasashen Estonia Letonia ta Lituania, sannan gobe juma´a, ya gana da shugabanin kasashen Polland Tchekoslovakia, Slovakia da Hongrie.
Babban burin wannan ziyara shine ,na neman goyan bayan kashen a yunkurin cimma daidaito, a game da kassafin assusun EU ,na shekara ta 2007 zuwa 2013.
Sauran kasashen Membobin kungiyar na zargin Britania da Fransa, na saka tarnaki da cimma daidaiton, a dalili da san kai da su ka nuna.