1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Tony Blair a gabas ta tsakiya

Yahouza S. MadobiSeptember 11, 2006

Praministan Britania Tony Blair na ci gaba da rangadi a yankin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/BtyJ
Hoto: AP

Tony Blair ya fara wannan rangadi da Isra´ila, inda ya tanttana da takwaran sa, Ehud Olmert a game da wajibcin komawa tebrin shawara da Palestinu, domin samar da hanyoyin shinfiɗa zaman lahia.

Manazarta harakokin siyasa, na danganta ziyara ta Tony Blair, a matsayin wani mataki, na farfaɗo da kwarjinin sa, a sakamakon tsaka mai wuya da ya shiga a halin yanzu, a ciki da kuma wajen Britania.

Bisa dukan alamu. Tony Blair ya cimma nasara kussanto ra´ayoyin ɓangarorin 2 , domin Ehud Olmert, da Mahamud Abbas, sun alƙawarta masa, komawa tebrin shawarwarin.

Praministan Isra´ila yayi wannan alƙawari kamar haka……………

„Ina mai nuna matukar shawar hawa rebrinshawara da mkwabtan mu Palestinawa“.

Kazalika, Olmert ya jaddada hakan a taron majalisar ministocin sa, da ya jagoranta jiya.

Shima a na sa ɓangare, shugaban Hukumar Palestniwa Mahamud Abbas, yayi na´am, da shawara tare da cewa:

„Yau a shire mu ke, mu tanttana da Praministan Isra´ila, Ehud Olmert, domin kawo ƙarshen wannan rikici.

A game kuwa da harakokin siyasar da ke wakana a Palistinu, Praministan Britania, ya bukaci girka gwamnatin haɗin kan ƙasa tsakanin ƙungiyar Hamas mai rinjaye a Majalisar Dokoki, da jam´iyar fatah.

Blair ya ci gaba da cewa:

„Mudun a ka girka wannan gwamnati, ina kyauttata zaton ƙasashen dunia za su damawa tare da ita“.

To saidai, ba da wata wata ba, kakakin Hamas Sami Abou Zouhri, ya yi watsi, da shawara Tony Blair, ta girka gwamnatin haɗa ka.

Ya ce Palestinawa ne, ya su yasu ,su ka fi kowa sannin abunda ya fi dacewa a gare su, a saboda haka, basa buƙatar shawara daga ƙasashen yammacin dunia.

A matakin gaba na wannan ziyara, yau Praminsita Tony Blair ya sauka a birnin Beyruth, na Libanaon, ya gana da hukumomin ƙasar, a game da tallafin Britania a ƙoƙarin sake gina ƙasar da hare haren Isra´ila, su ka yi ma kaca-kaca.

Shugabanin Schi´a na Libanon, da yan adawa, sun yi kira ga mogoya bayan su, su fito ƙwan su da kwalkwata ,domin shirya zanga zanagr nuna ƙin jinnin Tony Blair.

Su na zargin sa da marawa Isra´ila baya, a hare haren da da ta kai Libanon.

Kazalika sun tuhumi Tony Blair, da kasancewa a tsaka-tsakiyar shugabanin ƙasashen da su ka dabaibaye yunƙurin tsagaita wuta, a yaƙin da a ka gwabza tsakanin dakarun Hizbullahi da Isra´ila.

Wannan itace ziyara farko, da Praminsitan Britania, ya kai a yankin tun bayan yaƙin.

Tonny Blair,na gudanar da wannan ziyara, cikin tsautsauran mattakan tsaro, a birnin Beyruth da kewaye.