Ziyara Tony Blair a fadar gwamnatin Jamus | Labarai | DW | 17.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Tony Blair a fadar gwamnatin Jamus

Nan gaba a yau ne, shugabar gwammnatin Jamus Angeler Merkel, za ta karbi bakunci Praministan Britania, Tony Blair a fadar gwamnatin Jamus, dake birnin Berlin.

Wannan itace ziyara farko da Blair, ya kawo a Jamus tun bayan kaddamar da Angeler, a matsayin shugabar gwamnati.

Magabatan 2, za su tantana a kan batutuwa daban daban da su ka shifi, kungiyar gamaya turai, da hakin da ake ciki, a yankin gabas ta tsakiya, mussaman a dangane da rikicin nuklear Iran, da kuma nasara, da kungiyar Hamas ta samu, a zaben Palestinu.

A yamacin yau, Blair da Angeler Merkel, za su shirya taron manema labarai na hadin gwiwa, domin bayyana sakamakon ganawar ta su.