1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara tawagar ƙungiyar tarayya Afrika a Tchad

April 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv10

Tawagar ƙungiyar tarayya Afrika, na ci gaba da ziyara aiki a ƙasar Tchad, bayan rikicin da ya wakana tsakanin yan tawaye da gwamnati.

Shugaba Idriss Deby ya zargi Sudan da hannu a cikin harin yan tawayen, sannan, ya tuhumi ƙungiyar tarayya Afrika, da ƙin cewa uhum, a game da shiga sharo ba shunu, da Sudan ke wa harakokin cikin gidan Tchad.

Au ta tura wannan tawaga, domin samar da hujjoji na bayyanai, wanda ke nuna sa hannun Sudan a cikin rikicin.

Tawagar na da tsawan sati guda, domin gabatar da rahoton ayyukan ta, ga komitin tsaro na AU, wanda a ƙarshe, zai huruci a game da gasikiyar zargin, da kuma matakin da ya cencenta a ɗauka.

A wani labarin kuma, da ya shafi Tchad, a na ci gaba da tantanawa a birnin Washington, tsakanin tawagar gawmnatin kasar, da ta bankin dunia, a game da taƙƙadar da haɗa ɓangarorin 2.

A watan Janairu da ya gabata Bankin Dunia ta yake shawara saka takunkumi ga kuɗɗaden albarkatun man Petur, na Gwamnatin Tchad, bayan bankin ta zargi Gwamnati da pacaka da wannan dukia.