Ziyara shugabar Swuizland a Afrika
July 10, 2007Ita ma Shugabar tarayya Swuizland, Micheline Calmy-Rey, ta fara rangadi a wasu ƙasashe 7 na nahiyar Afrika.
A matakin farko, ta yada zango a ƙasar Benin,inda ta bayyanawa shugaban ƙasa, Thomas Yayi Bony gamsuwa, a game da girkuwar demokraɗiya da kuma hoɓa sarmar hukumomin Porto Novo, babban-birnin ƙasar, ta fannin yaƙi da talauci.
Micheline Calmy-Rey, ta ce demokradiyar ƙasar Benin abun koyi ce, ga sauran ƙasashen Afrika, a game da haka ƙasar ta cencenci samu ƙarfin gwiwa daga Swuizland.
Tawagogin ƙasashen 2, sun rattaba hannu a kann yarjejniyoyi da deama, fannin kiwon lahia, yaƙi da jahilci da kuma inganta tsarin mulkin demokradiya.
Bayan Jamhuriya Benin, shugaabr tarayya Swuizlana za ta kai raagadi a ƙasashen Ghana, Senegal, Tchad, Jamhuriya Demokradiyar Kongo, Burundi da Rwanda.