Ziyara shugaban kasar Iraki a Iran | Labarai | DW | 23.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara shugaban kasar Iraki a Iran

Shugaban kasar Iraki Jallal Talabani, ya kammalla ziyara aikin da da ya kai a kasar Iran.

Wannan ziyara da itace ta farko, da wani shugaban Iraki ya kai Iran, a tsawon shekaru 40, na da mahimmanci ga kasashen 2.

Tallabani da Ahmadu Nijad, sun yi anfani da wannan dama, inda su ka tantana batutuwa daban daban, da su ka shafi zaman lahia da tatalin arziki.

A yayinda su ka kiri taron manema labarai na hadin gwiwa shugabanin 2 sun nuna matukar gamsuwa agame da sakamakon wannan ziyara, da ko shakka babu, a cewar su, za ta kara karfafa danganta da alaka, na gadin gadin, da su ka hada al´ummomi da magabata Iraki da Iran.

Saidai jim kadan bayan wannan ganawa, majalisar dokokin iran, karro na 3 ta yi watsi da sunan mutumen da shugaba Mahmud Ahmadi Nidjad ya gabatar mata a matsayin ministan kulla da albarkatun man Petur.