1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara shugaban Isra´ila a kasar Italia

November 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvKj

Shugaban kasar Isra´ila, Moshe Katsav, na ci gaba da ziyara aiki a kasar Italia.

Jiya ya gana da shugaban gwamnati Silvio Berliskoni, inda su ka tantana a game da harakokin diplomatia tsakanin kasashe 2.

Berliskoni ya gabatarwa bakon na sa shawara, Isra´ila ta shiga sahun kasashen kungiyar gamayya turai.

A yayin da kiri taron manema labarai, Moshe Katsav ya yaba da wannan tayi, saidai yace Isra´ila ba ta yi tunani ba ya zuwa yanzu, a game da haka, duk da alaka da dangataka masu dogon tarihi, da su ka hada yahudawa da turai.

Nan gaba a yau, zai sadu da Paparoma Benedikt na 16, a fadar Vatikan, inda zai kai masa goran gayyata zuwa kasar Isra´ila.