1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara shugaban Iran a Venezuela da Bolivia

Shugaban ƙasar Iran Mahamud Ahmadinedjad, ya gana da takwarorin sa na Bolivia da Venezuela.

A matakin farko na wannan rangadi, Ahmadinedjad, ya tanttana da shugaba Evo Morales, na Bolivia a birnin Lapaz, inda su ka yi masanyar ra´ayoyi a kann batutuwa daban-daban da su ka jiɓanci mu´amila tsakanin ƙasashen 2.

A ƙasar Venezuela Hugo Chavez ya jaddada goyan baya ga ƙasar Iran a yunƙurin ta, na samar da makamashin nuklea, matakin da ke shan suka, daga ƙasashen dunia.

Chavez da Ahmadinedjad, sun rattaba hannu a kann yarjeniyoyi daban- daban, ta fannin makamashi, da albarkatun noma, kazalika, sun bayana matsayin su, na gama ƙarfi da ƙarfe, domin fuskantar ƙalubalen ƙasar Amurika.