1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara shugaban Brazil a Burkina Faso

October 16, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8N

Shugaban ƙasar Brazil, Luis Inacio Lula Da Sylva ,ya kai wata taƙaittata ziyara, a ƙasar Burkina Faso.

A yayin da ya gana da hukumomin Ouagadougou, Lula yayi kira ga ƙasashen Afrika, su himamantu, wajen yin anfani da makashin da ake samu ta hanyar kayan noma.

A cewar shugaban na Brazil ,yawaita yin anfani da wannan makashi a matasyin man petur cikin motoci da sauran ababen hawa, zai taimaka matuƙa wajen rage ɗumamar yanayi, tare da taka kyaukyawar rawa, ta fannin yaƙi da talaucin da yayi wa Afrika kanta.

Ƙasar Brazil a halin da ake ciki, na ɗaya daga ƙasashen dunia da su ka yi fice, ta fannin yin anfani da makamashi ta hanyar sarrafa ganyi rake.

A ɗaya wajen, Lula Da Sylva, ya tsokaci a game da rashin adalcin da ya ce ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ke nunawa masu tasowa, a game da harakokin saye da sayaraw.a.

A sakamakon wannan ziyara ta yini ɗaya, tawagogin Burkina Faso da na Brazil, sun rattaba hannu a kann yarjejeniyoyi ta fannoni daban-daban.