Ziyara shugaban ƙasar China a Saudiyya | Labarai | DW | 23.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara shugaban ƙasar China a Saudiyya

Bayan ƙasar Amurika da ya ziyarta a wannan mako, shugaban ƙasar China, Hu Jintao ,ya fara rangadi a Saudi Arabia.

A yayin da ya ke jawabi gaban komitin shura na ƙasar, Hu Jin Tao,ya bayyana mahimamancin yankin gabas tasakiya, a dandalin siyasar dunia, a game da haka, dunia ba zata taba samun ci gaba ba, muddun wannan yanki na fama da tashe tashen hankulla inji shugaba JinTao.

Ya ƙara da cewa, ƙasar China, a shire ta ke, ta bada haɗin kai, domin magance rigingimu iri-iri, da ke gudana a yankin.

A birnin ya gana, da shugaban komitin hulɗoɗi, na ƙasashen yankin Golf, inda su ka tantana, a kan batutuawa da su ka shafi rikici tsakanin Israela da Palestinu, da na makaman nukleyar ƙasar Iran, da kuma halin da ake ciki Iraki.

Kazalika, Hu Jin Tao, ya tantana da shugabanin kampanoni da masana´antu ,na Saudi Arabia , inda su kayi mansayar ra´ayo yi, a game da hanyoyin bunƙasa hulɗoɗin saye da sayarwa tsakanin ƙasashen 2.

Hukumomin Saudi Arabia, sun bayyana yiwuwar gina wani runbun tsimin man petur na mussaman a China, ta la´akari da cewar ita ke sahun na 2, bayan Amurika wajen anfani da man Petur a dunia.