1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara shugaba Jacques Chirac na France a kasar Thailand

Shugaban kasar France Jacques Chirac, ya fara ziyara aiki a kasashenn Thailand da India.

Tawagar Chirac ta kunshi manyan jami´an gwamnati, da ta kunshi ministocin tsaro da na cinikaya, da na harakokin ketare, da manya yan kasuwa na kasa.

A Thailand, Jacques Chirac zai gana a tsawonkwanaki 2 da hukumomin kasar, a game da batutuwa da su ka jibanci kasuwanci, da kuma diplomatia, tsakanin kasashe 2.

Wannan itace ziyara farko, da shugaban France ya kai, Thailand ,a matsayin sa na shugaban kasa.

Bayan Thailand zai ziyarci kasar India ranar lahadi mai zuwa.