Ziyara shugaba Hu Jintao na China a Vietnam | Labarai | DW | 31.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara shugaba Hu Jintao na China a Vietnam

Shugaban kasar China Hijintao ya sauka sahiyar yau a birnin Hanoi na Vietnam a wata ziyara aiki ta kwanaki 3.

Wannan itace ziyara ta farko da shugaban ya kai a Vietnam a matsayin sa na shugaban kasa.

Kasashen 2 za su anfani da wannan dama, domin karfafa mu´amilar cinikaya tsakanin su, da kuma kara daidaita diplomatia.

China da Vietnam sun samu rashin fahintar juna a shekara ta 1979 bayan da China ta kai hari ga Vietanam, dalili da mamayar da ta yi wa Kambojiya.