Ziyara Shinzo Abbe a ƙasar Amurika | Labarai | DW | 27.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Shinzo Abbe a ƙasar Amurika

Praministan ƙasar Japon, Shinzo Abbe, ya kai ziyara farko a ƙasar Amurika, inda ya gana yammacin jiya da shugaba George Bush.

Magabatan 2, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da hulɗoɗin diplomatia da na cinikaya tsakanin Amurika da Japon.

Kazalika, sun yi tantana game da rikicin makaman nuklear Corea ta Arewa da kuma Iran.

Shinzo Abbe, na ɗaya daga masu bukatar matsa ƙaimi ga hukumomin Pyong-Yang a dangane da buƙatar wasti da mallakar makaman nuklea.

Ya kuma samu tabbas, daga Gorges Bush na ƙara matsa lamba ga Corea ta Arewa, har sai lokacin da ta bada kai bori ya hau.