1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Sarkozy a Lybia

Shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy, ya sauka a ƙasar Lybia, a ziyara farko da ya kai, tun hawan sa kann karagar mulkin France, a watan mayu da ya gabata.

Wannan ziyara da ke wakana kwana ɗaya rak!!! bayan belin likitocin nan 6 da kotun Lybia ta yake wa hukunci kissa, na matsayin wata alama, ta daidaita mu´amila tsakanin Turai da Lybia.

Tun shekara 1988, ƙasashen turai da Amurika, su ka azawa Lybia karan tsana, a sakamkon zargin da su kewa shugaba Khaddafi, da ɗaurewa ta´adanci gindi.

Jim kaɗan bayan saukar sa Lybia, Sarkozy ya maida martani, ga masu zargin France da nuna alamomin sake ƙulla mu´amila da Lybia.

Bayan ƙasar Lybia, shuga Sarkozy, zai ƙasashen Senegal da Gabon, gobe da jibi, idan mai duka ya kai mu.