Ziyara Robert Gates a Irak
June 15, 2007Talla
Sakataran tsaron Amurika Robert Gates, ya kai ziyara ba zata a ƙasar Irak.
Gates ya gana da hukumomin Bagadaza, a game da batun hadin kan ƙasa da kuma kawo ƙarshen rikita-rikitar da ke wakana a sassa daban-daban na Irak.
Robert Gates ya bayyana matukar damuwa, a game da taɓarɓarewar al´ammura a ƙasar , inda a ko wace rana yan ƙunar baƙin wake, ke kai hare-hare, tare da hadasa asara mai tarin yawa.
Ziyara ta Robert Gates, ta yi daidai da ranar da wasu ƙarin sojoji 4 na Amurika su ka rasa rayuka a birnin Bagadaza.
Sanan wani jirgin sama, mai dura angullu mallakar rundunar Amurika, ya yi salla da ka, tare da sojan ɗaya a cikin sa.
Ya zuwa yanzu babu cikakar masaniya a game da mussabbabin faɗuwar wannan jirgi.