Ziyara Praminstan Iraki a Sa´udiyya | Labarai | DW | 30.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Praminstan Iraki a Sa´udiyya

Praministan kasar Iraki, Ibrahim Jafari, ya kai ziyara aiki a Sa´udiyya, inda ya gana da hukumomin wannan kasa, a game da riginginmun da ke wakana a Iraki, da kuma fadi ka tsahin da Sa´udiyya ke yi, na ganin an kawo karshen wannan tashe tashen hankulla.

A game kuwa da halin da a ke cikin a Iraki, kamar kullum yan kunar bakin wake ,sun ci gaba da kai hare hare.

A kalla mutane 10 ne, su ka rasa rayuka, daga wayewar sahiyar yau zuwa yanzu, a cikin hare hare daban daban.

A daya gefen kuma,yan takifen, na ci gaba da garkuwa da jami´an kasashen ketare da ke aiki a Iraki, inda a karro na farko, hadarin ya rutsa da wata bajamusa.

Yau ne kuma shugaba Bush, na Amurika zai gabatar da wani mahimin jawabi, wanda a cikin sa, zai bayyana matsayin gwamnatin Amurika, a game da kasar Iraki.

A bayan bayan nan, Shugaba Georges Bush, na fuskantar matsin lamba a cikin gida, daga masu adawa da wannan yaki, da, ya zubda kwarjinin Amurika, da na shugaban ta,da gwamnatin sa.