1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Praministan China a kasar Faransa

Praministan kasar China,Wen Jiabao, na ci gaba da ziyara aiki a kasar Faransa.

A sahiyar yau ya gana da takwaran sa Dominique De Villepin,a fadar sat a Matignon.

A sakamakon wannan ganawa China ta yi odar jiragen sama kira Air Bus, na jimilar kudade dalla billiyar 7.

A yayin da ya tantana jiya da babban manajan kampanin Air Buas a Faransa Praministan China ya bukaci masanyar hussa´o´i tsakanin China da Turai, a game da hikimomin kira jiragen sama.

A cikin hasashe da ya yi kampanin Air Bus, ya hango cewa, nan da shekaru 20 masu zuwa China za ta sayi a kalla jirage 2700 a wajen sa.