1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Paul Wolfowitz a Afrika

July 13, 2006
https://p.dw.com/p/Buqj

Shugaban bankin dunia Paul Wolfowitz na ci gaba da rangadi a wasu ƙasashen Afrika.

A birnin Addis Abeba matakin farko na wannan ziyara, ya bayyana cewar ci gaban ƙasar Ethiopia ya ta´alaƙa da kwanciyar hankali ta fannin siyasa.

Ya bayana hakan, a sakamakon tantanawar da yayi ,da Praminsita Meles Zenawi da kuma shugabanin jam´iyun adawa.

Wolfowitz ya yi hannun ka mai sanda, ga ɓangarori daban daban masu gaba da juna a ƙasar, a kan wajibcin shinfiɗa tsabttatar dangantakar siyasa, da girka demokraɗiya.

Bankin Dunia a cewar sa, ba zata saka kuɗaɗen ta ba, a ƙasar da babu kwanciyar hankali ta fannin siyasa, sannan wajibi ne, a kiyyaye haƙƙoƙin bani adama da shinfiɗa, alƙalanci cikin adalci, da yaƙar cin hanci da rashawa, wannan hanyoyin ne, da ke matayin rigar zamani, a saki ka huta, wanda kuma a kan su ne bankin dunia ta yi dogaro.

Nan gaba a yau ne Paul Wofowitz zai tashi zuwa Tanzania, zai ziyarci ɗaya bayan ɗaya ƙasashen Nigera, Benin, Sierra Leone, da Liberia.