Ziyara Paparoma a Poland | Labarai | DW | 28.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Paparoma a Poland

Shugaban ɗariƙar roman kaltolika na dunia, Paparoma Benedikt na 16, ya jagoranci wata gagaramar salla, a birnin Cracovie na ƙasar Poland ,inda ya ke ci gaba da ziyara.

Rahotani daga birnin sun ce, kussan mutane dubu 100, su ka halarci wannan salla, domin samun albarka daga shugaban addinin na krista.

A cikin huɗubar da yayi, gaban dubuanan jama´a, mabiya darika kataolika,Benedikt na 16, na mai cewa:

Ina gargaɗi ga matasan Poland, da na dunia, ku daina shan miyagun ƙwayoyi, dalili da mummunan illolin da ke tattare da su.

Masana harakokin shaye shayen ƙwayoyi a Poland, na dangata wannan ƙasa a matsayin ɗaya, daga ƙasashen da su ka yi ƙaurin suna, ta fannin shan miyagun ƙwayoyi, a nahiyar turai.

Kazalika ita ce ƙasa ta 2, bayan Holand, a jerin ƙasashen da ke sayar da miyagun ƙwayoyi a nahiyar turai.