1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyara paparoma a Landan

Paparoma Benedikt na 16 na cigaba da ganawa da dubban mabiya addinin Katolika a Birtaniya

default

Paparoma Benedikt na 16 na ganawa da jama´a a birnin Landan

Ɗalibai fiye da dubu biyu daga makarantun katolika na ƙasar Birtaniya suka hallara a ƙaramin garin Twickenham da ke wajen London, domin ganin Paparoma na 16 da idon u, wanda ke zaman abu mai matuƙar tarihi saboda a wurin, mafi yawancin su Paparoma wani ne wanda a Telebijin kawai a ke gani amma yau sun gashi gaba da gaba.

An daɗe ana zargin Paparoman da ƙyaliya dangane da jita-jitan luwaɗi a tsakanin limaman cocin na katolika da ma lalata da ake zargin su da yi da ƙananan yara, amma da saukar sa a tashar jirgin ya bayana wa 'yan jaridu takaicin yadda cocin ba ta ɗauki ƙwararan matakan da suka dace da wuri ba, wanda ake ganin babban cigaba ne tunda ya amince da cewan abu ne da ya kamata cocin ta mai da hankali a kai. Ko da ya ke a jawabin sa, ya ce kowa ya na da rawan takawa inda yace:

O-Tone Benedict

" Yanzu mu kan kwatanta addini da sauran ɓangarorin rayuwa da basu dace ba, don neman daidaito da sassauci, al hali kuwa addini shi ke tabbatar da daidaito da sassauci da yadda ma zamu mutunta juna kamar waɗanda suka fito da ciki ɗaya"

A yayin da mutane da yawa ke shigowa London daga wurare daban-daban domin su girmama wannan babban shugaban addini, wasu daga cikin mabiya ɗarikan na Katolika suna gudanar da zanga-zanga dangane da waɗansu manufofin cocin da basu amince da su ba.Waɗanda su ka haɗa da yadda cocin bata naɗa mata a matsayin limamai, ƙin amincewa da ɗaukan matakan samar da tazarar haihuwa da cocin ta yi dama masu fafutukan kare haƙƙin 'yan luwadi da maɗigo da ke zargin ana nuna masu wariya.  Duk da ce wa bai mai da martani game da waɗannan batutuwan kai tsaye ba, a jawabin sa ya yi magana kamar haka:

O-Tone Benedict

" Mu yi rayuwar da ke da daraja, akwai abubuwa da dama masu ɗaukan hankalin mutane daga tafarkin da ya kamata, musamman ma a wannan lokacin, kamar amfani da miyagun ƙwayoyi, kuɗi, jima'i da giya, waɗanda  ake ɗaukan su a matsayin kayan jin daɗi da faranta rai alhali su ne ke kai mutane ga hallaka"

Paporoman zai gana da majalisar dokokin Birtaniya a zauren majalisar  Westminister, daga nan kuma ana sa ran cewa Paparoman mai shekaru 83 zai gana da takwarar sa, shugaban cocin Angilika a fadarsa ta Cantebury, Arch-Bishop Rowan Williams. Shugabanin biyu sun haɗu a lokuta da dama, amma wannan ganawar da za su yi tana da mahimmanci da kuma tarihi saboda fadar da za su haɗu tana ƙarƙashin shugabancin cocin katolika kafin Sarkin Ingila Henry na Takwas ya raba ɗarikun biyu a shekarar 1534.

Mawallafi: Pinado Abdu

 Edita: Yahouza Sadissou Madobi