1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Osni Moubarack a Russia

Shugaban ƙasar Masar, Osni Mubarack, ya fara ziyara aiki a Russia.

A jawabin da yayi tare da yan jarida, shugaba Vladmir Poutine, na Russia, ya bayyana matuƙar farin ciki,da wannan ziyara, da zata ƙara daƙon zumunta tsakanin Mosco da Alqahira.

Shugabanin 2, sun tanatana batutuwa daban-daban, da su ka shafi , samar da makamashi da kuma makamai ga ƙasar Masar.

Sannan za su yi anfani da wannan dama, domin masanyar ra´ayoyi, a game da halin da ake ciki, a yankin gabas ta tsakiya.

A wannan ziyara ta kwanakji 3, Osni Mubarack, zai gana da shugabanin kamapanoni da masana´antu na ƙasar Russia

Osni Moubarack da yayi karantun soja tun shekara ta 1960 a Russia, ya yaba ƙurewar wannan ƙasa, ta fannin tsaro.