Ziyara Nuri Al Maliki a Syria | Labarai | DW | 21.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Nuri Al Maliki a Syria

A ciga ba da ziyara aikin da ya kai ƙasar Syria, praministan Iraki Nuri Al Maliki ya gana a yau da shugaban ƙasa Bashar Al Assad.

A tantanawar da yayi jiya da Praministan Irak, takwaran sa na Syria, ya bukaci Amurika ta bayyana tsarin fara janye dakarun ta daga Irak.

Praministan Syria Mohamed Naji Otri, ya nunar da cewa, ƙoƙarin da ƙasahse maƙwabtan Iraki ke yi, na samar da zaman lahia a ƙasar, ba zai cimma buri ba, sai in Amurika ta janye kwata-kwata daga Irak.

Nuri Al Maliki ya yi kira ga humumomin Damascus, su bada haɗin kai, don tabatar da zaman lahia mai ɗorewa a yankin baki ɗaya.

Amurika ta nuna rashin gamsuwa da ziyara Al-Maliki a Syria, ƙasar da gwamnatin shugaba Georges Bush ke ɗauka a matsayin mai fasa wutar rikicin Irak.

A watan Janairu da ya wuce, shugaban ƙasar Irak, Jallal Talabani, ya kai ziyara mako ɗaya a Syria, wadda itace irin ta ta farko da wani shugaban Irak, ya kai tun kimanin shekaru 30 da su ka gabata.