Ziyara Nuri Al-Maliki a Britania | Labarai | DW | 24.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Nuri Al-Maliki a Britania

Praministan ƙasar Irak Nuri Al Maliki, ya fara ziyara aiki ta farko a ƙasar Britania.

Nan gaba a yau zai gana da Praministan Tony Blair, inda za su tantana akan halin da ake ciki a Iraki.

Bayan London Nuri Al-Maliki zai wuce zuwa Amurika.

Saidai wannan ziyara na wakana a daidai lokacin da tashe tashen hankulla ke ci gaba da ƙamari a ƙasar Iraki.

A ƙalla mutane 70 su ka rasa rayuka, kussan 200 su ka ji mummunan raunuka, ranar jiya a cikin hare hare daban-daban da su ka wakana.

Dakarun Iraƙi, tare da na Amurika, sun kai wani samame a Sadr City, birnin da ke fama da yawan hare hare, daga yan yaƙin sari ka noƙe.

A nasa gefe, tsofan shugaban kasa Saddam a halin yanzu ya na kwance assibiti.

Rahotanin sun nunar da cewa, Saddam na fama da matsalolin lahia, bayan yajin ƙin cin abinci da ya fara, tun ranar 8 ga watan da mu ke ciki.

Yau ne kuma ake komawa, sauraran shari´a da ake yi masa.

Saidai lauyoyin sa da shi kansa Saddam Hussain,sun bayana ƙaraucewa zaman kotun.