Ziyara N .Sarklozy a Afrika
July 10, 2007Shugaba Nikola Sarkozy na France, ya kai ziyara farko a nahiyar Afrika, a matsayin sa na shugaban ƙasa.
A matakin farko Sarkozy ya ziyarci Algeria, ta la´akari da tarihin da ya haɗa France da wannan ƙasa.
Ya gana da takwaran sa, AbdulAziz Buteflika, inda su ka tantana, a game da al´ammura daban-daban da su ka jiɓanci tattalin arziki, diplomatia, da shigi da ficin al´umma, tsakanin Afrika da France.
Tawagogin ƙasashen2, sun tantana, a game da saye da sayarawa ta fannin makamashi.
Bayan birnin Algers shugaba Sarkozy, ya ta shji zuwa Tunisia.
A cewar kakakin fadar Elysee, babban burin wannan rangadi, shine gudanar da masanyar ra´ayoyi a game da burin shugaban ƙasar France a kann batun mu´amila tsakanin dukkan ƙasashen da ke ɓangarori daban-daban na gaɓar teku.