Ziyara Mohamed El Baradei a Amurika | Labarai | DW | 23.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Mohamed El Baradei a Amurika

Shugaban hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta Majalisar Dinkin dunia, Mohamed Albaradei, ya kai ziyara aiki a ƙasar Amurika, inda zai tanatana da sakatariyar harkokin waje Condolisa Rice a game da rikicin makaman nukleayer ƙasar Iran.

A makon da ya gabata, Mohamed El Baradei, ta sadu da shugaban tawagar Kasar Iran, Ali Larijani a game da rikicin.

Kamar sakatare Jannar na Majalisar Dinki Dunia, Mohamed Albaradei zai buƙaci Amurika, ta yi tantanawar ƙeƙe da ƙeƙe da hukumomin Iran a game da wannan batu mai sarƙƙaƙƙiya.

Saidai tun tuni Amurika tab sha maimaita manufar ta, ta watsi da wannan irin tayi, kamar yada su ma, hukumomin Iran, ke ci gaba da jaddada matakin sarafa makamashin Nukleya.

Saidai, masu kulla da harakokin diplomatia na dunia, na tunanin cewar, ziyara Albaradei a Amurika, ba za ta kawo wani cenji ba, a dangane da wannan rikici.