Ziyara M.Khadafi a Siera-Leone | Labarai | DW | 27.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara M.Khadafi a Siera-Leone

Shugaba Muhamar Khaddafi na Lybia, ya alkawarta bada tallafi mai tsoka ga al´ummomin ƙaasar Serla Leo, wanda yaƙi ya raunana, tsakanin shekara ta 1991 zuwa 2001.

Kahaddafi yayi wannan alƙawari albarkacin wata ziyara aiki da ya kai birnin Freeetown na ƙasar Siera Lene a jiya talata.

A jawabin da yayi gaba dubunan jama´a, a babban filin wasan ƙwalan Freetown, shugaban ƙasar Lybia, ya bayyana mahimmanci zaman lahia, a ci gaban ƙasashen dunia.

A lokacin yaƙin bassasar ƙasar Siera Leone an sha zargin Khaddafi da tura agaji ga yan tawaye.

A yau ne, Mohhamar Kahdafi ya kammala rangarin na ƙasar Siera Leone, a halin yanzu ya kan hanyar sa zuwa Cote d`ivoire.