Ziyara ministan harakokin wajen Jamus a yankin gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara ministan harakokin wajen Jamus a yankin gabas ta tsakiya

Ministan harakokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier, na ci gaba da ziyara aiki ,a yankin gabas ta tsakiya.

Bayan kasar Israela, da ya ziyarata jiya, ministan ya sauka yau, a Palestinu.

Tare da rakiyar takwaran sa, Nasser Al Qidwa sun ziyarci Ramallah.

Nan gaba a yau kuma, zai gana da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas.

Saidai, a cikin ajendar ta sa, babu batun ganawa ,da yan kungiyar Hamas, wanda za su girka sabuwar gwamnati, bayan nasara da su ka samu a zaben yan majalisun dokoki, na ranar 25 ga watan janairu da ya wuce.

Cemma, a ganawar da ya jiya, da Praministan rikwan kwarya na Israela, Steinmeier ya ambata cewa ba za shi gana ba, da kungiyar Hamas, muddun ba ta amince ba, da kwance damara yaki, ta kuma hau tebrin shawara da Israela, domnn warware rikicin gabas ta tsakiya cikin ruwan sanhi.

Kazalika ministan harakokin wajen Jamus, ya kiri dukkan kasashen dunia, da su mayar da Hamas saniyar ware, har lokacin da, ta ci ka sharrudan da kasashen su ka gindaya mata.