Ziyara ministan harakokin wajen Jamus a Latine Amurika | Labarai | DW | 01.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara ministan harakokin wajen Jamus a Latine Amurika

Ministan harakokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeir, ya fara wani rangadi a ƙasashen Latine Amurika.

Ya fara wannan ziyara da ƙasar Chili, kamin ya ci gaba zuwa Argentina da Brazil.

Babban bayyanin da ya ke ɗauke da shi, ya ta´allaƙa da shiryen-shiryen taron ƙoli, da zai haɗa ƙasashen ƙungiyar gamaya turai, da na Latine Amurika, daga 11, zuwa 12 ga watan da mu ke ciki a birnin Vienna.

A ɗaya gefe kuma, zai masanyar ra´ayoyi, da hukumomin wannan ƙasashe, da shugabanin kampanoni da masana´antu, a kan batutuwa, da su ka shafi harakokin saye da sayarwa, tsakanin Jamus, da ƙasashen kudancin Amurika.

A matakin farko na wannan ziyara, zai gana yau litinin, da yan kasuwar Chili, sannan ya haɗu gobe talata, da shugabar ƙasar Chili, Michelle Bachellet.

Zai kammalla rangadin ranar juma´a, bayan ya sadu da shugaban ƙasar Brazil, Lula Da Silva.