Ziyara mataimakin sakatare Janar na Majalisar Dinkin Dunia a Ethiopia da Erytrea | Labarai | DW | 12.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara mataimakin sakatare Janar na Majalisar Dinkin Dunia a Ethiopia da Erytrea

Mataimakin Sakare Janar na Majalisar Dinki Dunia,Jean marie Gueheno, yace har yanzu, akwai barazanar tsunduma saban yaki, tsakin Ethiopia da Erythrea.

A game da haka, yayi kira ga komitin Sulhu na Majalisar , da ya dauki matakan ladabtar da hukumomin kasashen 2.

Gueheno yayi wannan huruci a sahiyar yau bayab wata ganawa da yai da Pramionistan Ethiopia Meles Zenawi.

Duk da cewa hukumomin kasashen 2, na fadi da fatar baki cewa, ba za su koma ba fagen daga, bai issa hujja ta nuna masu sako sako, mussamman ta la´akari da yada su ke shiryen shiyre ta fannin soja.

Idan dai ba a manta ba,a makon da ya gabata ne, kasar Erythrea ta umurci, wasu membobin tawagar Majalisar Dinkin Dunia, da su fita daga kasar ta.

Ita kuwa Ethiopia ta sanar janye yawan dakarun ta a iyaka da Erytrea.