1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Mahmud Azhar a wasu ƙasashen nahiyar Asia

May 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bux2

A yau ne ministan harakokin wajen Palestinu, ya fara rangadin sati 2, a ƙasashen Asia.

Mahamud Azhar, zai ziyarci ,Indonesia, Malaisia, Sri Lanka da kuma Iran.

A karshen wannan rangadi, zai halarci taron hulɗoɗi tsakanin ƙasashen larabawa da China, da za ayi a birnin Pekin.

Ƙasar Isra´ila, ta rubuta wasiƙa ga gwamnatin China, inda ta bayana rashin gamsuwa, da gayyatar gwamnatin Hamas da ta yi, a wannan taro.

Babban burin da Palestinu ke bukatar cimma ,a ciki kai da kawon ministan ta, na harakokin waje, shi ne ciwo kan kasashen dunia, domin su bada tallafi, ga hukumar palestinawa, wada a halin yanzu ke cikin matsanacin karancin kuɗaɗen aiki, a sakamakon takunkumin da Amurika, da Tarayya turai, su ka saka mata.