1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Mahamud Azhar a Lybia

May 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv06

Ministan harakokin wajen Palestinu, na ci gaba da rangadi a ƙasashen larabawa, da zumar samar da agajin kuɗaɗen tafiyar da ayyuka.

Hukumar Palestinawa, ta shiga wani saban yanayi na matsalolin kuɗaɗe a sakamakon shawara da Amurika, da kasashen turai su ka yanke, ta tsuke bakin aljihu, ga gwamnatin Hamas.

A jiya Mahamud Azhar ya gana da shugaba Khaddafi na ƙasar Libiya.

Wannan ziyara, ta biwo bayan wata makamanciyar ta, da shugaban ƙungiyar Hamas, Khaled Michael ,ya kai Libia, a watan Maris da ya wuce.

Saidai ya zuwa yanzu, babu wani cikaken bayyani, a game da sakamakon wannan ziyarce ziyarce.

A ci gaba kuma da rikicin yankin gabas ta tsakiya, sojojin Isra´ila, sun harbe wata mata da sanhin sahiyar yau, a garinTulkarem, da ke arewa ga kogin Jordan.

Daga ɓarkewar yaƙin Intifada, a shekara ta 2000, wannan shine cikon mutun na 5.035, da ya rasa rai daga ɓangarorin 2.