1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Mahamud Abbas a Syria

January 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuTv
Condoleeza Rice
Condoleeza RiceHoto: AP

Shugaban hukumar Palestinawa, Mahamud Abbas, na ci gaba da rangadi, a wasu ƙasashen larabawa, inda ya ke tantanna batun samar da zaman lahia, a yankin gabas ta tsakiya , da kuma masalaha, a rikicin cikin gida, tsakanin ƙungiyoyin Fatah da na Hamas.

Bayan birnin Amman a ƙasar Jordan, da ya ziyarta juma´ar da ta wuce , a ranar jiya, Abbas, ya gana da takwaran sa, na Syria Bashar Al-Assad.

Tantanawar da su ka yi, ta maida hankali kaco-kam ! a kan matakan samar da sulhu, tsakanin Fatah da kuma Hamas, da ke gaba da juna, a Palestinu.

Saidai sabanin yadda aka tsara da farko Abbas bai sadu ba da Khaled Michael, Shugaban ƙungiyar Hamas, da ke gudun hijira a ƙasar Syria.

Jim kaƙan kamin ganawa, da hukumomin Damascos,Mahamud Abbas, ya tantanna da sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, Havier Solana, a kan rikicin Isra´ila da Palestinu.

Bayan birnin na Damascos, zai ci gaba da wannan ziyara ranekun 22 ,da kuma 23 ga watan Janairu, zuwa ƙasar Libanon.