1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Kondalisa Rice a yankin gabas ta tsaykiya

Yahouza SadissouNovember 14, 2005

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Kondalisa Rice na ci gaba da ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/Bu4D
Hoto: AP

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Kondolisa Rice na ci gaba da ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya.

A wannan ziyara da ta kai, Rice ta gana a yau da Praminista Isra`ila Ariel Sharon, inda su ka tantana a kan batutuwan da su ka safi aiki da taswirar zama lahia, da a ka cimma daidaito a kan ta, tsakanin Isra`ila da Palestinu da kuma dakatar da ginin matsugunai, da yahudawa ke yi a yankunan Palestinawa.

Ta gayyaci hukumomin Isra`ila, da su guji dukkan ayyukan da kan iya maida hannun agogo baya, ga yunkurin da a ka shiga na samar da zaman lahia a yanki da ke fama da tashe tashen hankulla.

Sharon ya jaddada matsayin sa, na ba zai koma ba tebrin shawara da Palestniwa muddun ba su yi maganin hare haren da kungiyoyin Hamas ke kai wa Isra`ila ba.

A daya hannun, Kondolisa Rice, ta tantana da shugaban hukumar palestinawa, Mahamud Abbas, inda a nan ma, batun zaman lahia, ya mamaye ajendar taron.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika, ta bukaci hukumomin Palestinu, su dauki mattakan da su ka dace, domin hana yan kungiyoyin Hamas, da na Jihadil Islami, kai hare hare ga Isra`ila, wanda hakan ne, ke hadasa kon gaba, kon baya, da a ke fuskanta a yunkurin cimma zaman lahia mai dorewa, a yankin gabas ta tsakiya.

Rice, ta jaddada matsayin Amurika na ganin an girka kasa mai cin gashin kann ta, ta Palestinu da za ta zaman girma da arziki da makwabciyar ta, Isra´ila.

Kodolisa Rice, ta hallarci tarrurukan da a ka tanadar, a birnin Kudus, domin tunni da cikwan shekaru 10, da kissan gillar da wani dan kunar bakin wake ,ya yi wa tsofan Praministan Isra`la Izak Rabin.

Nan gaba a yau ne, Sakatariyar harakokin wajen Amurika za ta zuwa Jordan, domin kai ta´aziya, ga hukumomin kasar bayan mace macen, da su ka abku a sakamakon hare haren ranar laraba da ta wuce.

Kamin wannan ziyara wakilin mussaman na Amurika a yankin gabas ta tsakiya, James Wolfensohn, ya tantana da bangarorin 2, a kan maganar zirga zirga tsakanin zirin Gaza da Masar ta hanyar yankin Rafah.

Ziyara ta Kondolisa Rice ta zo, daidai lokacin da rundunar tsaron Isra`ila,ta bayyana bindige shugaban yan yakin sunkuru na Hamas a Naplouse Amjad al_Hinnawi, sahiyar yau litinin.

Hukumomi Isra´ila, sun bayyana kame wasu mutane 8 a cikin arangamar da ta biyo baya.

Mutuwar Hinnawi ta kara hauda yawan mutanen da su ka rasa rayukan su, a cikin yakin Intifida zuwa 4.884, daga farkon wannan yaki a shekara ta 2.000 ya zuwa yanzu.