Ziyara Koffi Annan a gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 29.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Koffi Annan a gabas ta tsakiya

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, na ci gaba da ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya, a yunƙurin sa, na ƙarfafa zaman lahia tsakanin Isra´ila da Libanon.

Bayan ziyara da ya kai jiya a birninBeruth Annan ya ziyarci a sahiyar yau, dakarun Majlisar Ɗinkin Dunia, a kudancin ƙasar, kamin ya zarce zuwa Isra´ila.

A ganawar da yayi jiya, tare da hukumomin Libanon, Koffi Annan, ya yi kira ga Hizbullahi, ta sallami sojojin Isra´ial 2 da ta kame , sannan ita kuma Isra´ila, ta ɗage takunkumin hana zirga zirga, ta kuma hita daga wasu sassa na Libanon.

A cen birnin, New York na ƙasar Amurika, ƙasashen da su ka alƙawarta tura dakarun a kudancin Libanon, sun shirya zaman taro, inda su ka tantana a kann mattakan cimma nasara wannan aiki.

A jnimilce ƙasashe 30 su ka bayyana bada gudunmuwar sojoji acikin wannan runduna, da ta ƙunshi dakaru dubu 15.

A na ta ɓangare ministar harakokin wajen ,Isra´ila ta kawo ziyara a nan ƙasar Jamus, inda ta yi kira ga hukumomin Berlin, su sa baki, domin belin sojoji 2, na Isra´ila, da yan Hizbullahi su ka yi garukuwa da su.