Ziyara Koffi Annan a Cote d´Ivoire | Labarai | DW | 06.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Koffi Annan a Cote d´Ivoire

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan, ya gana da magabatan ƙasar Cote d´Ivoire, a ziyara aikin da ya kai a wannan ƙasa ta yammacin Afrika, da ke fama da rikicin tawaye.

A sakamakon taron da ya jagorata a birnin Yamouscouro, Koffi Annan, ya nunar da cewa, a watan Satumber mai zuwa, Majalisar Ɗinkin Dunia zata zaman taro na mussamman a kan makomar mulkin riƙwan ƙwaryan na shugaban Cote d´Ivoire Lauran Bagbo.

Taron, ya yanke shwara girka wani komiti wanda zai bi diddiƙin kwance ɗamara yaƙi, daga ɓangarori masu gaba da juna.

A hira da ya yi da manema labarai , Koffi Annan, ya bayyana gamsuwa da sakamakon da taron ya haifar, to saidai, ya nuna damuwa a kan ƙarancin kuɗaɗe da kan iya zama ƙalubale ga cimma dukan matakan da su ka tsaida.

Amma ta la´akari, da kaukayawar nasara da a samu, a yunƙurin maido da zaman lahia,a Ivory Coast, Annan ya kyauttata zaton, ƙasashe masu hannu da shuni, za su bada taimakon kuɗaɗen da su ka dace,don cimma burin da a ka sa gaba.