Ziyara Koffi Annan a Cote D´Ivoire | Siyasa | DW | 06.07.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyara Koffi Annan a Cote D´Ivoire

A sakamakon ziyara aikin Koffi Annan a Cote d´Ivoire, an ƙara samun ci gaba a yunƙurin warware rikicin ƙasar.

default

A ziyara aiki da ya kai jiya, ƙasar Cote D´Ivoire,Sakatare jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia Koffi Annan,ya jagoranci wani mahiman taro, da ya haɗa ɓangarori daban-daban masu gaba da juna, a birnin Yamouscouro.

Mahalarta taron sun yi bitar halin da ake ciki, a yunkurin maido zaman lahia a ƙasar, da kuma shirye-shiryen zaɓɓuɓukan da a ka ambata yi, a watan oktober na wannan shekara.

A sakamakon mahaurorin da a ka tabka, taron birnin Yamouscouro, ya cimma matakai da dama, wanda Annan ya fassara a matsayin babban cigaba a warware rikicin Cote d´Ivoire.

A wata hira da yayi da manema labarai, Koffi Annan ya ce Majalisar Ɗinkin Dunia, zata tantnawa, a watan satumber mai zuwa, a game da makomar mulkin riƙwan ƙwarya na shugaban Cote d´Ivoire Lauran Bagbo.

Tun watan oktober, na shekara ta 2005 wa´adin mulkin Bagbo ya kawo ƙarshe, amma, Majalisar Ɗinkin Dunia ta umurce shi, ya ci gaba, har lokacin da aka zaɓi saban shugaban ƙasa.

Mahalarta taron Yamouscouro, sun yi lalle marhabin da tantanawa a kan wa´adin mulkin shugaba Bagbo da Majalisar za ta yi.

Sanarwar karshen taron ta ƙara da cewa, kwance damara yaƙi da ruguza ƙungiyoyin sakai masu makamai, ya zama wajibi, mudun a na bukatar cimma zamanl ahia mai ɗorewa.

A game haka sun amince da girka komitin haɗin gwiwa kamin,15 ga wannan wata,wanda a aka ɗorawa yaunin bin diddiƙin kwance makaman.

Baki ɗaya ɓangarorin sun cimma daidaito, a kan gaggauta rijistar jama´ar ƙasa, domin tantance yawan mutanen da ya cencenta, su kaɗa ƙuri´u a zaɓɓuɓukan da za shirya.

Ɓangarorin, sun alkawartawa Koffi Annan, ajje makamai da kuma bada haɗin kai, wajen shirya zaɓen.

A nasa gefe, shugaban ƙasa Lauran Bagbo, ya amince ya damƙa aikin tafiyar da kwance ɗamara ga praminista riƙwan ƙwarya Charles konnan Banny , wanda ya samu kyaukyawan yabo daga Majalisar Ɗinkin Dunia saboda ayyukan da ya gudanar.

Sassan yan tawaye da na gwamnati, da kuma jam´iyun siyasa, sun yi na´am, su girka hukumar zaɓe mai zaman kanta, kamin ƙarshen wannan wata.

Saidai mahalarta taron ba su ce komai ba, game da yiwuwar dage zaɓen, kamar yada Koffin Annan ya yi hasashe a birnin Banjul ranar asabar da ta gabata.

Sakatare Jannar na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya bayana wannan tantanawa, a matsayin ci gaba ingantace, ta fannin samar da zaman lahia, da hauda Cote d´Ivoire, bisa turbar demokradiya, to saidai a ɗaya wajen ya bayyana zullumi, ta la´akari da ƙarancin kuɗaɗe da ake fuskanta, don cimma wannan buri.

Saidai Annan yayi kira, ga ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa, da ƙasashe masu hannu da shuni, da su taimaka da kuɗaɗen da su ka dace.

A yayin da Koffi Annan ke bayyana gamsuwa ,da wannan ganawa, su kuwa manazarta a kan harakokin siyasa, a Cote d´Ivoire cewa su ke, ba giringirin ba dai ta yi mai, domin so da dama, an sha cimma mataki irin wannan, amma a wayi gari,ɓangarori masu gaba da juna,kwanaki ƙalilan, su manta da alkawuran da su ka ɗauka, kuma ciwo ya koma ɗanye.

 • Kwanan wata 06.07.2006
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtzN
 • Kwanan wata 06.07.2006
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtzN